Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa sojoji na ci gaba da samum nasara a kan mayakan Boko Haram.

Hakan na dauke ne cikin wani jawabi da mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau  ya gabatar a wani taro tare da Hafsoshin Tsaroda aka gudanar a ranar Lahadi.

A cewar Gwamnan, a baya bayan nan sojoji sun samu nasarar kwato makamai daga hannun masu tayar da kayar bayan a garin Gwoza.

“Wannan ya nuna yadda karsashi da jajircewar sojoji wajen samar da zaman lafiya, wanda ya kamata mu ci gaba da ba su kwarin gwiwar don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa,” a cewar Zulum.

Kazalika, Bataliya mai lamba ta uku ta rundunar Operation Lafiya Dole, ta yi galaba kan wasu mayakan Boko Haram ranar Juma’a a kauyen Jigalta da ke kan hanyar Monguno zuwa Gajiram.

Aminiya ta samu rahoton cewa, sojojin Bataliya ta 112 a garin Mafa, sun kwato wata babbar mota cike da makamai da babura hannun ‘yan ta’adda a kan hanyar Monguno zuwa Gajiram.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: