Matashin Likitan Najeriya Ya Rasu Bayan Kamuwa da Zazzabin Lassa Daga Wurin Mara Lafiya

0 156

Al’ummar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bingham (BHUTH) da ke Jos, Jihar Plateau, sun shiga jimami bayan rasuwar wata matashiyar likita, Dr. Salome Oboyi, wadda ta rasu ranar Litinin, 2 ga Fabrairu, 2026, bayan ta kamu da zazzabin Lassa daga wani mara lafiya da take kula da shi.

Wani sako da Kungiyar Likitocin Alumni na Jami’ar Bingham ta wallafa a shafinta na X ya tabbatar da cewa kafin rasuwarta, Oboyi ta kasance Babbar Likitar zama (Senior Resident) a sashen kula da mata masu juna biyu da haihuwa (Obstetrics and Gynaecology).

Sanarwar ta ce rasuwarta ta girgiza daukacin al’ummar asibitin, inda abokan aiki, abokai da marasa lafiya suka nuna alhini, suna tuna ta a matsayin likita mai sadaukarwa, kwarewa da kuma hidima ba tare da son kai ba.

Leave a Reply