Mawuyacin Halin Da Wata Sakandire Ke Ciki A Jigawa

2 217

Babban burin kowacce al’umma mai tunanin cigaba a rayuwa bai wuce samar da ilimi mai nagarta ga jama’arta ba, amma sai dai abin mamaki shi ne yadda shuwagannin da suka ɗauki rantsuwar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu suke shakulatin ɓangaro da nauyin da ya rataya a akansu.


Jihar jigawa dai kamar yadda kowa ya sani shi ne ilimi na cikin halin ni ƴa su a dalilin rashin bashi kulawar da ta kamata. Hakan ta sanya sauran jihaho suka fara yi mata nisa. Sai Mahunkun sun zage damtse sosai matuƙar suna son kai jihar ga gaci.


Yanzu haka dai wata Makarantar gaba da Firamare dake Garin Gwaram mai suna GDJSS Gagaryaga Gwaram a sakamakon lalacewa da ajujuwan karatunsu suka yi . ga kuma yanayin da ake ciki na damina.

Wanda hakan ya tilastwa malaman Makarantar gudanar da darrusa tare da ɗalibansu a karkashin bishiya ko kuma tantagaryar fili.


Wasu masu kishin Yankin nasu da wannan matsalar ke faruwa Musa Magaji da Nasiru Gwaram sun wallafa hotunan a shafukansu na Facebook yadda ɗaukar karatun yake gudana a fili kamar a karnin na 16 farkon zuwan ilimin zamani.

“Yadda ake gabatar da darusa a gindin bishiya a makarantar GDJSS Gagaryaga Gwaram a sakamakon rushewar Ajinjiwan karatunsu. Muna kira ga GwabnatiJiha data Samar da Sabin ajinjiwan a makarantar duba da yanayin da muke cikin na damina.”

  1. musa says

    Salam. Barkada hutawa babu abinda xance shine Allah ibakh

  2. Rabiu abdu gwaram says

    Gaskiya neh Amma akwai Dan gyara, yadda lamarin yake shine aranar lahadi 13/05/2019 misalin karfe 4:46 pm dayagabata Allah ya kawo ruwa da iska Mai qarfi Wanda yayi sanadiyyar rushewa ajujuwa uku da Kuma ofishin malamai a wannan makaranta da Kuma gidajen dake kewayanta da suka hada da gidan wani mutum Mai qaramin qarfi Mai suna hussaini Mai gidan gamji da Alh kabiru haruna Mai buhu, Kuma wannan matsala tuni a matsayin Yan kwamstin SBMC na wannan makaranta mun sanarwa da hukumar da ta dache Wanda har tsohon sakataren ilmin alh abdu madaki ya Kai ziyarar Jake wurin da abun ya faru

Leave a Reply

%d bloggers like this: