Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun tare matafiya tare da yin awon gaba da su da bakin bindiga a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

0 218

Mayakan kungiayr ISWAP sun tare matafiya tare da yin awon gaba da su da bakin bindiga a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a yau Asabar.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da adadin matafiyan da kungiyar ta yi garkuwa da su ba a harin na misalin karfe 8.30 na safiya a yankin Benisheik.

Majiyar tsaro a yankin ta tabbatar da aukuwar lamarin,

Majiyar ta ce matafiyan na hanyarsu ta zuwa Maiduguri daga Damaturu ne mayakan na ISWAP suka tare su bayan sun wuce Benisheik suka tafi da su zuwa inda ba a sani ba.

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula a Yankin Arewa maso Gabas, Ambasada Ahmed Shehu, ya tabbatar da labarin garkuwa da matafiyan.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto babu wani bayani a hukumance game da harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: