Mayaka masu ikirarin jihadi sun halaka sojojin kasar Burkina Faso 53 a wata arangama

0 239

Akalla sojojin kasar Burkina Faso 53 aka halaka a wani arangama da suka yi tsakanin su da mayaka masu ikirarin jihadi.

Mummuna lamarin ya faru ne ranar litinin yayinda sojojin kasar suka kawai mayakan hari.

An gwabza fadan ne a yammacin gundumar Yatenga, inda sojojin kasar ke kokarin kwace iko da shi.

Tun a shekarar 2015 Kungiyoyin mayaka masu ikirarin jihadi dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda ke kai hare-hare a Kasar ra Burkina.

An halaka mayaka masu ikirarin jihadi da dama, yayinda aka jikkata sojojin kasar 17 da kuma wasu fararan hula 36.

Shekaru biyu da suka gabata, an yi juyin mulki sau biyu a kasar mai makwabtaka da Mali da Jamhuriyar Nijar. Sojojin da sukayi juyin mulki sunce sun kwace ikon kasar ne sabida yawaitar hare-haren kungiyoyin Jihadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: