An kaddamar da kwamitin tsaro da zaman lafiya na Manoma da Makiyaya na karamar hukumar Guri

0 241

Gwamna Malam Umar Namadi ya kaddamar da kwamitin tsaro da zaman lafiya na Manoma da Makiyaya na karamar hukumar Guri, wanda zaiyi aiki domin samar da zaman lafiya da kuma yin sulhu dangane da rikicin da ake samu tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma a karamar hukumar.

Gwamnatin jihar Jigawa ce ta samar da kwamitin domin samu mafita da magance matsalolin tsaro, da kuma tabbatar da dorewar tsaro a karamar hukumar Guri,ta hanyar samar da wuraren noma da kiwo domin kowa ya gudanar da aikin sa yadda aka tsara,ba tare da take hakkin wani ba.Kwamitin, na da Mambobi da suka hada shugabannin gargajiya, jami’an tsaro da yan sa kai, da kuma shugabannin al’umma, nada ka’idodji 11 da za’ayi aiki karkashin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: