Muddin aka kasa cimma matsaya kungiyar kwadago NLC zata tafi yajin aiki na gama-gari

0 300

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC reshen Jihar Jigawa ta bi sahun takwarorinta na kasar nan wajen shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu

Shugaban kungiyar na jiha, Comrade Sanusi Alasan Maigatari ya ce hakan na daga cikin matakan da ake bi domin ceto al’umma daga halin da suke ciki sakamakon cire tallafin man fetir.

Ya ce gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu zai bada dama domin tattaunawa da Gwamnati, muddin aka kasa cimma matsaya uwar kungiyar zata tafi yajin aiki na gama-gari

Comrade Sunusi Alhassan Maigatari wanda ya yabawa ma’aikatan jihar Jigawa bisa bin umarnin kungiyar na tafiya yajin aiki na kwanaki biyu, ya bada tabbacin cewa za su yi dukkan mai yiyuwa domin samar da mafita ga ma’aikata da kuma al’ummar kasa baki daya. Tafiya yajin-aiki gargadin ya yi tasiri bisa la’akari da yadda aka gudanar da shi a sassa daban daban na kasar nan wanda hakan ke nuna cewa, akwai yiyuwar a koma tebirin sulhu tsakanin gwamnati da uwar kungiyar kwadago ta kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: