Har yanzu muna mafarkin samarwa Nijeriya ci gaban da ta ke bukata – GEJ

0 113

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya roki ‘yan Nijeriya da kada su sare a ganin ci gaban kasar nan.

Jonathan ya ce har yanzu akwai kyakyawan fatan ganin mafarkin samarwa Nijeriya ci gaban da ta ke bukata.

Yayin da yake tsokaci a kan bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai, Jonathan ya ce a daidai lokacin da jama’ar Nijeriya ke jinjina wa shugabannin farko, yana da muhimmanci a mayar da hankali wajen bayar da gudumawar da ake bukata domin habakar kasar.

Tsohon shugaban kasar ya ce a karon farko an kwashe shekaru 25 ana gudanar da dimokiradiya ba tare da matsala ba, tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999.

Kazalika, ya ce matakin ya bayar da damar samun ci gaban tattalin arziki da hadin kan jama’a.

Jonathan ya ce duk da yake ana fuskantar wasu manyan kalubalen da suka hana kasar samun ci gaban da ta ke bukata ta fuskar tsaro da tattalin arziki, yana da matukar muhimmanci a karfafa hukumomin kasa wadanda za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro.

Tsohon shugaban ya kuma bukaci masu rike da madafun iko da su tabbatar da gaskiya da adalci a kowane mataki, musamman wajen raba mukamai da arzikin kasa, tare da bai wa matasa damar shiga ana damawa da su. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: