Matatar Dangote za ta taimaka wa Afirka wajen fita daga talauci

0 106

Dr. Mohamed Ibn Chambas, kwararren dan diplomasiyya kuma wakilin Tarayyar Afirka a shirin “Silencing the Guns,” ya bayyana cewa, Matatar Mai ta Dangote, wanda ke da karfin tace ganga 650,000 na danyen mai a kowacce rana, wani babban shiri ne da zai taimaka wa Afirka wajen fita daga talauci.

A ziyara da ya kai matatar da ke Ibeju Lekki a Jihar Lagos, Chambas, ya jaddada cewa Kamfanin Dangote na jagorantar bangaren ‘yan kasuwa masu zaman kansu a Afirka, yana mai ba da misali da hangen nesan Aliko Dangote da kuma kwarewar Najeriya.

Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan tabbatar da samun isasshen man fetur ga Matatar Dangote, yana mai cewa Tinubu ya nuna jajircewa wajen ƙirƙirar ingantaccen yanayin kasuwanci a Najeriya. Ibn Chambas ya yi kira ga ‘yan Afirka da su ziyarci Matatar Dangote don ganewa idanunsu gagarumin cigaban da aka samu ba ga Najeriya kadai ba, har ma ga dukkan Afirka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: