Buhari ya bayyana jin daɗinsa kan hukuncin da kotun ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke

0 258

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana jin daɗinsa kan hukuncin da kotun ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke.

Wanda ya tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan Fabrairu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar, Mallam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce kotun ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasar ta “kafa tarihi” ta hanyar yin watsi da duk wata barazana da zarge-zarge marasa tushe wajen yanke hukunci cikin gaskiya da adalci, don martaba zaɓin ‘yan Najeriya.

Buhari ya ce “duk wanda ya yi nasara a yau dimokraɗiyya da al’umma ne suka yi nasara, idan Kotun Ƙoli ta yanke hukunci, to an gama da batun zaɓe lokaci ne da ya kamata ƙurar zaɓe ta kwanta”.

Muhammad Buhari yace gwamnatin APC ƙarƙashin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta samu goyon bayan kowa domin cika alƙawuran da ta ɗaukar wa al’umma.

Toshon shugaban ƙasar ya kuma aike da saƙon taya murna ga shugaban ƙasar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da kuma jam’iyyar APC kan wanna nasara da suka samu a kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: