Miji Ya Harbi Masoyin Matarsa da Kibiya

0 32

Miji ya harbi masoyin matarsa da kibiya

Ana zargin wani magidanci da harbin masoyin matarsa da kibiya a yankin Ƙaramar Hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ce magidancin mai shekara 22 ya harbi matar tasa ne bayan wata taƙaddama da ta ɓarke a tsakaninsu a kusa da gidan iyayenta.

Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce an kai rahoton lamarin hedikwatar ’yan sanda ta Tarmuwa, inda aka fara gudanar da bincike.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya tarar da matarsa a cikin wani yanayi na rashin dacewa tare da wani mutum a kusa da gidan iyayenta da ke ƙauyen Danewa-Biriri.

A cewar ’yan sandan, a sakamakon haka, rikici ya ɓarke tsakanin mutanen biyu, inda ake zargin mijin matar ya harbi ɗayan da baka da kibiya, lamarin da ya jikkata shi sosai.

Abdulkarim ya ce wanda aka harba yana karɓar magani a Asibitin ’Yan Sanda da ke Damaturu, yayin da aka kama wanda ake zargin.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru, kafin ɗaukar matakin shari’a da ya dace.

Da yake tsokaci kan lamarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Yobe, Usman Kamfani Jibrin, ya gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

Ya buƙaci jama’a da su riƙa kai rahoton duk wata taƙaddama ko aikata laifi ga ’yan sanda domin a warware su ta hanyar da doka ta tanada.

Leave a Reply