Ministan wutar lantarki yayi bayanin dalilan da suka jawo karancin wutar lantarki a ‘yan kwanakin nan

0 88

Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, yayi bayanin dalilan da suka jawo karancin wutar lantarki a ‘yan kwanakinnan, inda ya lissafa karancin ruwa a lokacin rani da aikin gyra da ake yi a kamfanonin samar da gas.

Tun daga watan da ya gabata, sassan kasarnan da dama ke fuskantar karancin wutar lantarki.

Ministan a wajen taron manema labarai jiya a Abuja, yace ana magance matsalar dauke wutar da ake fuskanta a fadin kasarnan ta hanyoyi daban-daban.

Domin magance kalubalen, ministan yace gwamnati na aiki wajen kara yawan gas din da ake samarwa domin bangaren wutar lantarki ta hanyar bayar da kwangiloli.

Ya kara da cewa za aci tarar kamfanonin da aka ba wa kwangila muddin basu aiwatar da abinda ya kamata ba.

Ya kuma ce za a samu karin wutar lantarki domin tabbatar da wadatar wutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: