Akwai ‘yan Najeriya kimanin 300,000 dake gudun hijira a Jamhuriyar Nijar

0 93

Kwamishiyar tarayya ta hukumar kula da ‘yan gudun hijira, Imaan Sulaiman Ibrahim, tace akwai ‘yan Najeriya kimanin dubu 300 dake gudun hijira a jamhuriyar Nijar.

Tace akwai wasu dubu 20 a Chaid da dubu 180 a Kamaru, amma adadin zai iya raguwa kasancewar an fara aikin dawo da su gida.

Ta kuma ce an fara sanya ido akan ayyukan kungoyiyi masu zaman kansu domin magance cin amanar aikinsu a guraren da ake rikici.

Imaan Sulaiman Ibrahim, yayin wata ziyara zuwa helkwatar kamfanin Media Trust a Abuja dake wallafa jaridar Daily Trust da Aminiya, tace an bawa ma’aikatar jin kai, kula da annoba da walwalar jama’a ikon amincewa da ayyukan kungoyiyi masu zaman kansu, domin su dace da kudirorin gwamnati.

Ta kara da cewa matsalolin kungoyiyi masu zaman kansu sun sanya wasu gwamnatocin jihoshi kin amincewa da ayyukansu a jihoshinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: