Kamfanin sadarwa na MTN ya bayyana cewa ya samu ribar Naira biliyan 414 a cikin watanni shida na farkon shekarar 2025 a Najeriya.
Rahoton kudin shiga da kamfanin ya gabatar a gaban Hukumar Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya (NGX) ya nuna cewa duk da samun wannan riba, kamfanin ya tafka asarar Naira biliyan 90 sakamakon canjin kudaden kasashen waje.
A cewar rahoton, jimillar kudin shiga kafin cire riba ya kai Naira tiriliyan 1.2. Kudaden da suka fito daga kiran waya sun kai Naira biliyan 887, yayin da kudin shiga daga amfani da intanet (data) suka kai Naira tiriliyan 1.23.
Kamfanin ya alakanta wannan ci gaba da yanayin kasuwanci a Najeriya, wanda ya hada da daidaituwar darajar Naira da kuma saukar farashin kayayyaki.