Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mutum 16 a wani samame da ta kai wasu sassan birnin Kano kan zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa tarbiyya.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Mujahiddeen Aminuddeen ya ce mutanen da aka kama sun haɗa da maza shida da mata 10.
A cewarsa, an gudanar da samamen ne a El-Kanemy Suite da ke kan titin Yahaya Gusau da kuma wasu wurare a hanyar BUK, Danbare da Layin Shisha.
Ya ce, ana yi wa waɗanda aka kama nasiha tare da gayyatar ’yan uwansu domin wayar musu da kai, kafin su rattaba hannu kan alkawarin daina irin waɗannan ayyuka.
Aminuddeen ya ƙara da cewa, Hisbah za ta ci gaba da sa ido a kansu bayan an sake su domin tabbatar da sauyin hali.