Muna daf da samar da isasshiyar wutar lantarki – KEDCO

0 60

Turakun Samar da wutar Lantarki a Kasa baki da ya sun sake katsewa a jiya wanda hakan ya janyo an samu rashin wutar sau 3 cikin wata daya a kasa baki daya.

A ranar 14 ga watan Maris da misalign karfe 10:40 na safe ne aka samun matsalar daukewar wutar lantarkin a kasa baki daya.

Haka kuma a ranar 15 ga watan Maris din ne aka sake samun katsewar wutar lantarkin a kasa baki daya.

Da yake tabbatar da gaskiyar lamarin cikin wata sanarwa, Shugaban Sashen Sadarwa na Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki shiyar Kaduna Malam Abdulazeez Abdullahi, ya ce a jiya wutar lantarkin ta sake katsewa da misalin karfe 6:29 na yamma.

Haka kuma kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Abuja, ya tabbatar da gaskiyar labarin cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya Juma’a.

Wannan na zuwa ne kasa da wata daya, bayan gwamnatin tarayya ta sha Alwashin daukar matakai domin magance matsalar wutar lantarki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: