

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Majalisar Dattawa ta amince da kudirin kafa Jami’ar Sufuri ta Tarayya da ke Daura a Jihar Katsina.
Jami’ar da aka warewa kudi dalar Amurka miliyan 50, tuni aikin ginta ta ya kai kashi 50 cikin 100.
An zartar da kudirin ne yayin zaman majalisar na jiya bayan ‘yan majalisar sun yi la’akari da rahoton kwamitin kula da manyan makarantu da TETFUND.
Dan majalisar ta dattawa daga jihar Oyo, Abdulfatai Buhari ne ya dauki nauyin kudirin na neman samar da dokar da ta kafa jami’ar, wacce ya bayyana a matsayin irinta ta farko a Najeriya da Afrika.
A yayin karatu na biyu, sanatan ya ce jami’ar za ta kiyaye da tabbatar da dorewar dimbin jarin da gwamnatin tarayya ke zubawa a fannin sufuri.