Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kudi naira miliyan dubu 35 domin gudanar da ayyuka daban-daban a fannin sufurin jiragen sama

0 76

Majalisar zartarwa ta tarayya jiya a Abuja ta amince da kudi naira miliyan dubu 35 domin gudanar da ayyuka daban-daban a fannin sufurin jiragen sama.

Ayyukan sun hada da karin kudin gina tasha a filin jirgin saman Akanu Ibiam na jihar Enugu da filin jirgin saman Asaba.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya bayyana haka bayan taron majalisar ministocin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya.

Ya ce an amince da naira miliyan dubu 5 da miliyan 600 na kudaden domin kula da sabbin gine-ginen kasa da kasa a filayen jiragen saman Abuja da Fatakwal.

Ministan ya kara da cewa an amince da kudi naira miliyan dubu 14 da miliyan 700 domin gina asibitoci a tashoshin jiragen sama na Abuja, Kano, Fatakwal, da Legas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: