Sabon fada ya barke yau a kudancin jamhuriyar demokradiyyar Congo, kwanaki bayan ‘yan tawaye sun ayyana tsagaita wuta domin bayar da damar tattaunawa da gwamnati.

Cikin kwanaki kadan da suka gabata, kimanin ‘yan gudun hijira dubu 6 ne da suka koma gida a jamhuriyar demokradiyyar Congo suka sake tserewa zuwa kasar Uganda dake makotaka.

Majiyoyi sun ce dakarun gwamnati na fada da nufin sake kwace iko da kauyukan dake lardin North Kivu wanda a halin yanzu suke karkashin ikon ‘yan tawaye.

Ana sa ran shugabannin yankuna zasu gana a wannan makon domin tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye.

A wani labarin kuma, kungiyoyi 2 na hakkin bil’adama sun zargi dakarun soji daga yankin Amhara na kasar Habasha da kaddamar da gangamin kisan kiyashin kabilanci ga ‘yan Tigray.

A wani rahoton hadin gwiwa, Amnesty International da Human Rights Watch sun zargi jami’an Amhara da dakarun yankin na musamman da ‘yan bindigan dake yaki a yammacin Tigray da aikata laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil’adama.

Kungiyoyin sun kuma zargi dakarun sojin Habasha da hannu cikin laifukan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: