PDP tana kan matsayar ta na bawa kowanne dan takara tikiti ba tare da duba shiyyar sa ba

0 63

Kwamitin karba-karba na jam’iyyar PDP ya bayar da shawarar bayar da dama ga kowane dan takara daga kowace shiyyar kasarnan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

An cimma matsayar hakan yayin zaman kwamitin da aka gudanar jiya a Abuja.

Idan kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya amince da shawarar, ‘yan takara daga kowace shiyyar kasarnan zasu iya tsayawa takarar kowane mukami, ciki har da kujerar shugaban kasa.

An rawaito cewa kwamitin, karkashin jagorancin gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, ya ambaci karancin lokacin a matsayin dalilin matsayar da suka cimma.

A halin da ake ciki, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da sabon gargadi ga jam’iyyun siyasa akan kauracewa amfanin da jadawalin hukumar na zaben 2023.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar a jiya, hukumar tace baza ta lamunci duk wani yunkurin jam’iyyun siyasa ba na yin watsi da matakan da kundin tsarin mulki ya gindaya wajen tsayar da ‘yan takara gabannin zaben cikin gida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: