

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya gargadi mazauna jihar da su guji gini akan hanyoyin ruwa da cinye filayen da aka bari a gefen sabbin titunan da aka gina.
Inuwa Yahaya, yayi gargadin ne yayin zantawa da manema labarai a jiya, jim kadan bayan yayi rangadin duba wasu ayyukan titunan cikin gari da ake ginawa.
Gwamnan yace an biya diyyar filayen, inda yayi bayanin cewa gwamnatin jihar tayi aniyar amfani da su wajen shuka bishiyoyi da sanya fitilun gefen hanya masu amfani da hasken rana tare da gyara bututun ruwa domin wadatar ruwan sha, da sauransu.
Gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da matakin ayyuka da ingancin dukkan ayyukan titinu da ake gudanarwa tare da nanata jajircewar gwamnatinsa wajen tabbatar da nasarar ayyukan gwamnatinsa.
Tunda farko, kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar, Engineer Abubakar Baffah, yayi bayanin cewa titin mai tsayin kilomita 4.3, daya ne daga cikin aikin titunan birnin Gombe kashi na 6.