Munci galabar rashin tsaro tunda mun yaki Boko Haram – Gwamnatin Tarayya

0 80

Gwamnatin tarayya tace kasarnan tana cigaba da samun tsaro kowace rana sanadiyyar nasarorin da ake samu a yaki da Boko Haram da ISWAP da ‘yan fashin daji da sauran bata gari.

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, shine ya sanar da haka yayin taron manema labarai jiya a Abuja.

Yace dakarun tsaro suna fatattakar ‘yan fashin daji inda suke rage musu karfi kowace rana.

Kazalika, gwamnatin tarayya tace karuwar farashin wasu kayayyakin abinci da fetur da man disel da sauran kayayyaki, duniya ya shafa gabadaya ba Najeriya kadai ba.

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya sanar da haka yayin taron manema labarai jiya a Abuja, ya kara da cewa mayar da lamarin na Najeriya kadai yaudara ce da kokarin yada labaran karya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: