Mutane 5 Sun Hallaka, Wasu Da Yawa Sun JIkkata

0 210

Mutane biyar ne suka rasa rayukansu yayin da gidaje da dama suka kone kurmus biyo bayan wani rikicin da barke tsakanin yan kabilar Tiv da Jukun, a yankin Rafinkada dake karamar hukumar Wukari a jihar Taraba.

Kantoman ruko na karamar hukumar Mr Daniel Adidas ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa a birnin Jalingo.

Ya ce wasu yan bindiga sanye da kayan sojoji suka budewa mazauna garin na Rafinkada wuta, sannan suka kone gidaje da dama.

Soja guda ya samu Rauni yayin harin inda aka meka shi asibitin Wukari domin duba lafiyarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: