Mutane 822 Ne Suka Mutu, Yayin Da Wasu Mutane Dubu 3 Da 215 Suka Jikkata Yayin Rikicin Sudan

0 95

Kungiyar likitocin kasar Sudan ta bayyana cewa adadin fararen hula da suka mutu sakamakon fadan da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojoji da dakarun kungiyar RSF ya kai 822, yayin da wasu mutane dubu 3 da 215 suka jikkata.

Rikicin da ya barke a ranar 15 ga watan Afrilu ya kara tabarbarewa duk da tattaunawar sulhu da aka yi a birnin Jeddah mai tashar jiragen ruwa na kasar Saudiyya da kuma sanya hannu kan yarjejeniya a ranar 11 ga watan Mayu domin kare fararen hula da samun damar kai musu kayayyakin agaji.

A cewar likitocin, sauran biranen da fararen hular suka mutu a rikicin sun hada da Khartoum babban birnin kasar da kuma biranen Bahri da Omdurman da ke makwabtaka, sai kuma El Obeid, babban birnin jihar Kordofan ta Arewa. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, rikicin da ya shiga wata na biyu, ya kuma raba kusan mutane miliyan guda daga gidajensu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: