An Sake Gano Wasu Gawarwaki 10 Na Masu Azumin Yunwa A Dajin Da Ke Gabar Tekun Kasar Kenya

0 118

An sake gano wasu gawarwaki 10 a dajin da ke gabar tekun kasar Kenya inda aka ce an sanya mutane sun mutu sanadiyyar yunwa bayan sun shiga wata kungiyar asiri.

Wannan ya kawo adadin gawarwakin mutane 211 da aka gano yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da binciken wadanda suka mutu.

Bayan hutun kwanaki biyu, an ci gaba da aikin gano gawarwakin a dajin mai girma sosai a jiya.

Daga cikin karin gawarwakin da tawagar masu binciken gwamnatin ta gano akwai yara biyu.

An ceto wasu ’yan kungiyar asirin su uku a cikin wani mawuyacin hali bayan da yunwa ta lahanta su a Dajin, inda aka kai su asibiti domin ceto rayukansu.

Wadanda aka bayar da rahoton bacewarsu a lamarin sun kai 610.

Leave a Reply

%d bloggers like this: