Mutane da dama sun mutu a wata girgizar kasa a kasar Haiti

0 113

Akalla mutane biyu ne suka mutu a wata girgizar kasa mai karfin maki 5.3 da ta aukawa kudu maso yammacin kasar Haiti a safiyar jiya.

A wani karamin gari dake gabar ruwa mai nisan kilomita 130 daga babban birnin kasar, wata mata ta mutu lokacin da wata katanga ta rushe. A wani garin kuma, mai nisan kilomita 20 kudu da babban birnin, an samu mutuwar wani sanadiyyar zaftarewar kasa.

A lardin Nippes, wanda girgizar kasar tafi kamari, kimanin gidaje 200 ne suka rushe yayin da wasu gidajen kimanin 600 suka lalace, a cewar hukumar kare rayukan fararen hula.

Masu aikin ceto sun bayar da rahoton cewa kimanin mutane 50 ne suka jikkata.

A watan Augusta, a wata girgizar kasa mai karfin maki 7.2 ta kashe mutane sama da dubu 2 da 200 tare da lalata gomman dubban gidaje a kasar da har yanzu ke kokarin farfadowa daga wata mummunar girgizar kasa da ta auku a shekarar 2010.

Leave a Reply

%d bloggers like this: