Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Yiwa Ɓarna A Jigawa Sun Samu Tallafin NEMA

0 271

Hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa NEMA ta bayar da kayan amfani gona ga mutane 9,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2018 a karamar Hukumar Kirikasamma da ke nan Jihar Jigawa.

Jami’in yada bayanai na yankin Alhaji Sanusi Doro shi ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin Labarai hakan a garin Kirikasamma a ranar Litinin.Jami’in kula da rabon kaya na Ofishin NEMA Mr Olanrewaju Kazir ya sanar da cewa, akwai ayyukan da suke gudana a jihar domin ganin an magance ambaliyar ruwa da ake fama da ita a jihar.

Kowanne daga cikin wanda ambaliyar ruwan ta shafa, wadanda yawancin su Manoma ne, sun karbi buhun shinkafa mai nauyin Kilogiram 40, da kuma iri, da abin feshi da roba daya na maganin kwari da kuma roba daya na sinadarin kasha tsirran da ba’a bukatar su a gona.

Mr Olanrewaju ya kuma bada tabbacin cewa nan gaba kuma za’a bayar da buhuhunan taki guda tara ga dukkannnin wadanda lamarin ya shafa, idan suka bada shaidar abin amfanin da aka basu.

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ruwan da ta faru a shekarar da ta gabata ta 2018 tayi sanadiyyar mutuwar mutane 21, tare da shafar sama da garuruwa 200 da ke jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: