Mutum 4 ’Yan Gida Daya Sun Mutu Bayan Ruftawar Bene A Kano

0 78

Mutum 4 ’yan gida ɗaya sun mutu bayan ruftawar bene a Kano

Mutum huɗu ’yan gida ɗaya sun mutu, yayin da wasu 12 suka jikkata sakamakon ruftawar wani bene mai hawa biyu a unguwar Ɗandinshe Kwanar Yashi da ke Ƙaramar Hukumar Dala a Jihar Kano.

Ginin, mallakin wani mutum mai suna Yusuf Officer ne, kuma shi ne yake zaune a cikinsa tare da matansa uku da ’ya’yansa 12.

Wani mazaunin yankin, Abubakar Garba Ibrahim, ya ce ana kan aikin hawa na biyu na ginin kafin su ruftar da ta auku a ranar Asabar.

Ya ce an ceto mutane huɗu daga cikin waɗanda ginin ya rufta a kansu suna raye, amma a sume, kafin daga bisani su rasu.

Ya ƙara da cewa mazauna yankin da jami’an ceto sun shafe kusan sa’o’i tara suna aikin ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.

A cewarsa, a halin yanzu ana kula da waɗanda suka jikkata a wani asibiti.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an ceto mutum 13 da ransu.

Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce sun samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 4:32 na asubahin Asabar daga wani ma’aikacinsu, Aminu Sani Warure.

Abdullahi ya ce nan take aka tura jami’an hukumar zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka ceto mutum 13, ciki har da yara, da ransu.

Ya ce daga cikin waɗanda aka ceto akwai Al-Mustapha Yusuf, mai shekaru 15; Khadija Yusuf, mai shekaru bakwai; Ummusalama Yusuf, mai shekaru 10; Madina Yusuf, mai shekaru shida; da Hafsat Yusuf, mai shekaru tara, da wasu mutum takwas waɗanda ba a samu sunayensu nan take ba.

Kakakin hukumar ya ce an miƙa dukkan waɗanda aka ceto ga Usman Ibrahim, wanda yake ɗan uwan mahaifinsu, domin a ci gaba da ba su kulawar lafiya.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin ruftawar ginin.

Ya kuma shawarci mazauna yankin da su ƙara yin taka-tsantsan musamman a lokacin nan na damina, domin kauce wa sake faruwar irin wannan mummunan lamari.

Leave A Reply

Your email address will not be published.