Najeriya na neman dala biliyan 25 don gina bututun gas zuwa Turai – Shettima

0 90

Najeriya na neman dala biliyan 25 a matsayin kuɗin aikin shimfiɗa bututun gas zuwa nahiyar Turai.

Mataimakin Sugaban Najeriya kashim Shettima ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da shugaban kamfanin Vitol Group a fadar shugaban ƙasa ranar Litinin.

Aikin bututun wanda zai bi ta ƙasar Morocco, za a yi amfani da shi wajen sayar wa ƙasashen Turai iskar gas, yayin da suke yunƙurin rage dogaro da Rasha a fannin makamashi.

Mataimakin shugaban ya nemi masu zuba jari na ƙasashen duniya da su antaya kuɗaɗensu a Najeriya, yana mai cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu “na aikin saita Najeriya”.

Leave a Reply