Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta samu nasara kan kasar Burundi a wasan farko na rukuni na gasar cin kofin nahiyar Afrika a jiya.
Najeriya dai ta lallasa su daci 1 mai ban haushi ta hannun dan wasanta Ighalo bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
A yanzu dai Najeriya nada maki 3 a rukunin ta.