Yadda Tsohon Gwamna Ya kashe fiye da Biliyan 23 wajen binne gawarwaki- Gwamnan Bauchi

0 82

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi zargin cewa tsohon gwamnan da ya gada, Mohammed Abubakar ya kashe fiye da Naira Biliyan 23.3 a wajen binne gawarwaki.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Dokta Ladan Salihu, wanda ya gana da manema labarai a Bauchi a ƙarshen mako.

Salihu ya ce an kashe Naira Biliyan 23.3 tsakanin watan Janairu da Mayu, 2019.Ya ce an kashe fiye da Naira Miliyan 900 wajen siyan likafani, yayinda aka kashe fiye da Biliyan 1.4 wajen siyan itatuwan da ake ɗorawa a kan kabari bayan an binne gawa.

A cewar mai magana da yawun Gwamnan, lokacin da gwamnati mai ci ta karɓi mulki ta gano batutuwan cin hanci, venality da yadda aka yi wadaƙa da dukiyar al’ummar jihar da tsakar rana, kuma tana kan bincikar abubuwan da suka faru a gwamnatin da ta gabata.

“Kuɗin da ya kamata a ce Majalisar Dokokin Jihar nan ta amince da su kafin a kashe su, kwatsam sai suka ɓata daga litattafanmu na lalitar gwamnati.“Ya za a yi a ce Gwamnatin Jiha, a cikin wata biyar, wato tsakanin Janairu da Mayu, 2019 ta kashe fiye da Naira Biliyan 23.3 wajen siyan kayan jana’iza, likafani da itatuwan da ake ɗorawa a kan ƙaburbura?”, Dokta Salihu ya tambaya.

Da aka tambaye shi ko gwamnati mai ci tana da hujjojin da za ta kare wannan iƙirarin nata, Salihu ya ce babu kokwanto game da wannan batu, yana mai ƙarawa da cewa akwai shaidun da za su iya tabbatar da haka.

Ya ce: “Dukkan waɗannan abubuwa suna cikin rahoton Kwamitin Karɓar Mulki, kuma an tattaro waɗannan abubuwan ne daga takardu, takardun biyan kuɗi, da kuɗaɗen da aka biya daga litattafanmu na lalitar gwamnati.

“Akwai Dokar ‘Yancin Samun Bayanai.“Yi amfani da ita ka gano wa kanka daga waɗancan takardu”, in ji shi.Salihu ya ce duk wani kwabo da aka kashe ba bisa ka’ida ba za a gano shi, yana mai ƙarawa da cewa gwamnati mai ci za ta cuna wa duk wanda ake zargi Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC da Hukumar Hukunta Laifuka Masu Alaƙa da Cin Hanci Mai Zaman Kanta, ICPC don su bincike shi.

“Gwamnati za ta ɗauki ƙwararan matakai.“Za mu gano duk wani kwabo da gwamnatin da ta gabata ta yi almundahanarsa ko ta sace, da ma gwamnatin da ta gabace ta.

“Indai muka tabbatar da cewa ga rashin bin ka’ida a fili wajen kashe kuɗi, wajibi ne mu bincika.“Ba za ka bari a ci gaba da aikata laifi ba ba kai ba gindi saboda kuɗin gwamnati ne”, a kalaman Dokta Salihu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: