Dalilai 12 Da Kansa Mata Tsanar Jinin Al’ada, Na 7 Yafi Ciwo

0 205

Al’adar mata ko batan wata wani lokaci ne da yake faruwa da jinsin halittar mutane mata dake cikin rukunin wasu shekaru na yan matanci da kuma girma kafin manyanta.


A wannan yanayin ne mata ke tambayar kansu wai mai yasa nake yin wannan abin? Mai yasa sai mu mata kadai?
To amma ga maganar gaskiya, al’ada abu ne maras dadi, mai matukar cin rai wanda yake sanya kyakkywar rayuwar matan dake rukunin shekarun cikin kunci. Su kan ji kamar su zabi su daina da za’a tambaye su. Su kan ji rayuwarsu tafi dadi a baya kafin su fara (balaga).

Hoto: Healthfacts


Ya mai karatu babban makasudin wannan rubutu shi ne shailantawa duniya irin halin da yan uwanmu mata ke shiga na wasu yan kwanaki a duk watan duniya.


Hanya mafi dacewa ta hucewa idan kana cikin halin damuwa shi ne ta hanyar tattauna da mutanen da ke fuskantar irin halin da kake ciki, ta haka zaku yi musayar ra’ayi da irin salon da matsalar tazo muku da shi, watakil ku samarwa kanku mafita ko shawara mai bullewa ga juna.


Amma dai kafin muyi nisa akwai abu mai muhimmanci da ya kamata mu sani wanda shi ne; ke mace ce kuma dole ki yarda haka tsarin halittar mace yake. Daga lokacin da kika karbi haka a matsayin tsarin rayuwa to daga nan ne kika karbi kaddarar tsarin matuntaka. Amma ba abu ne da mata zasu kunyarsa ba ko boye kansu kamar masu laifin da ake nema ruwa a jallo.


Hakan ta sanya yau nayi nazarin wasu daga cikin abubuwan da kansa mata tsanar zuwan jinin al’adar tasu duk da dai watakil ba iya dalilan kenan ba, hakan bai rasa nasaba da cewa ni Namiji ne bana yinta ko kuma karancin ilimi a fannin domin har yanzu cikin koyo nake.

Alamun zuwa (1)


Wannan wasu alamomi ne dake nuni da cewa bako na hanya sauran kirin ya karaso, wadannan alamomi yawanci na farawa ne mako guda kafin zuwan al’ada. Wani abin ban mamaki da dariya game da bakon wata shi ne; sau tari yakan zo ne da wasu kananun damuwa masu birkita rayuwar mata.


Da farko wasu matan kan fuskanci matsananciyar yunwa kamar zasu ci babu, ciwon kai, ciwon baya da kuma kaikayin mama mai matukar damu wanda har kan sanya amfani da rigar mama yin wahala a wasu lokutan.


To mazaje idan saboda kallon kurilla kun iya gano wata bata sanye da rigar mama sai kuyi mata uzuri watakila wannan matsalar ce ke faruwa da ita. Ina sane da fitinannun yan matan nan da basu son a zauna lafiya, wannan sashinsu daban ne.

Alamun zuwa (2)


Bayan duk kin cinye abubuwan dake cikin na’urar sanyi, (fridge) ko Burodin da ya kamata yayi muku kwana 2, kin yi ta shan magungunan rage radadi (painkillers) yanzu kuma lokaci yayi da al’adar zata wajiga rayuwarki da sanya ki fara zama kamar wata kwarkwar.


Zaki fara abubuwa cikin fushi da bacin rai ga duk wanda yayi miki Magana babu gaira ba dalili ko kuma ki rinka jin ke komai ya gundire ki kamar ki ma daina aiki ko kawai ya sake ki. Hahahaha yar uwa dama kin gane kin saurara domin wannan duk alamu ne kafin gwaskan yazo! (a rubutu na gaba zan fadi lakanin maganin wannan matsalar).

Karuwar Kaurin Jiki


Kwatsam babu zato ba tsammani sai kiga kin fara karuwa kamar fulawar da aka zubawa sinadarin kumburi (yeast) amma kada ki damu idan hakan yana faruwa dake domin kawai wani ruwa ne da wasu sinadarai da suka wanzu a kasan fatarki, zasu sabe. Zulumbuwar ki da tayi maki kadan zata dawo ta na shigarki.


Digar Jini


Wani dalilin dake sanya mata tsanar zuwan bakonsu shi ne digar jini, komai kaurin kunzugu (auduga) (pad) mata da yawan gaske sunyi asarar kayansu masu kyau watakil sabo ko wanda suka fi so ta dalilin wannan digon jinin, amma karki damu yar uwa da yazo babu kunzugun gara ya digo (collateral damage) ya kike gani idan yazo babu audugar al’adar?

Zabin Mummunan Lokacin Zuwa
Wani hali da yake gundurar mata shi ne lokacin zuwan bakon, sau tari ya kanzo ne a daidai lokacin da ba’a zaton zuwansa ko kuma bai kamata ya zo ba.

Kawai sai ki ga abu ranar jarrabawa ko cikin taron mutane ko akan hanya ko kuma kin tafi unguwa kai har fa yakan iya zuwa lokacin da kika je neman aiki (job interview) ko yayin zantawa da saurayi. wallahi duk kadan ne daga aikin wannan bakon.

Yar boye


Shi fa wannan bakon yakan iya yin wasan buya, yazo ya labe ya tafi ya dawo. Hakan kuma sai ya tilasta an dangana da likita don tabbatarwa ko komai lafiya da kuma jin dalilin kin zuwan wannan bako, musamman idan budurwa ce da bata son daukar ciki kuma taga bai zo ba, ai kuwa da matsala, e mana to ya zata yi tun da dai bata yi komai ba kuma bakon da zai tabbatar da hakan yaki yayi bayani ta hanyar zuwa. Idan yazo hakan na nufin babu juna biyu.

Soke Duk Wani Shiri


Sau tari zuwan wannan bako kan janyo sokewa ko daga halartar wani muhimmin taro. Wasu kan zafi zama a gida don kawai su suka san irin yadda suke ji ko kuma tsoron jizgawa a gaban mutane, tunda ba shi da tabbas. Wasu lokutan kudin sayen audugar ma kadai kan jefa rayuwar mata cikin tunani.

Zuwa Ba Kakkautawa


Wannan karon zuwa ba da wasa yake ba! Idan kina daga cikin rukunin matan da suke fuskantar hakankin san mai nake nufi. Zuwa yake yi kamar ka matse bakin bututu, idan irin hakan ta faru kuwa shawara ta gare ki karki tsaya ko ina sai gida ko gidan kawa ko yan uwa mafi kusa. Maza ruga!

Jawo Jin Kunya


Hakan na faruwa ne kasancewar kin tashi kin ga saura audugarki 1 tal ko kuma an je siyowa ba a samo ba don haka dole a tafi neman aro, yawanci ga kawayen da ke zaune wuri guda aron auduga (Pad) ba wani sabon lamari ba ne musamman dalibai.

Rashi Audugar Al’ada Mai Kyau Ko Tsadarta


Samun audugar al’ada mai kyau daidai yake da samun ruwan sanyi a lokacin matsanancin kishi, yawanci ko dai ki samu tayi laushi sosai ko kuma mau tauri kababa wanda hakan ke takurawa gaban mata, su ji babu dadi har su na tambayar kansu wai mai ke faruwa ne?


Kamar dai yadda idan ka sanya suturar da tayi maka yawa ko ta matseka kake ji.
Wata audugar kuma na dauke da sinadarai masu karfi (chemicals) da ka iya jefe rayuwarsu (gabansu) cikin hadari ko kuma audugar tayi tsada ta yadda wasu matan kan gaza siya, musamman ga masu karamin karfi.

Asarar Jini mai yawa


Bakon wata na mata kan sanya zubar jini mai yawa fiye da yadda maza ke tunani, za dai mu iya cewa daidai yake da mazuka jini (vampires) har ma wasu masu irin wannan matsalar ta zubarsa da yawa kan fuskanci karancin jini.

Sai dai kash ba abu ne da za a iya magancewa ta hanyar cin tuwo ba ko kuma abinci maras gina jiki ba, don haka matan da basu samun abinci mai Karin jini suke cikin hadari.

Zagwanyewar Kyau


A can baya nayi makamancin wannan batun, sai bambancinsa da wannan shi ne, yawanci ga wasu matan sai ya sauya masu kamanni musamman a fuska ko fatar jiki ko kumburin kafa

Gyara (Bonus)


Kara kyau (Pigmentation)
Matan da ke kara kyau yayin al’ada basu da yawa, ga wasu matan tabon da yayi makonni bai bace ba ko wasu bakaken kuraje da zarar bakonsu yazo yakan bace bat.


Dalilan ba zasu kirgu ba musamman a cikin gajeren rubutu irin wannan haka zalika su kan bambanta a tsakanin mata, wasu nasu daban ne.

Mu hadu a rubutu na gaba mai taken Dalilin da yasa mata ke yin jinin al’ada
Kuyi min uzuri idan nayi kure ko a gyara min

Abubakarsd@live.com

Leave a Reply

%d bloggers like this: