Nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya zasu ga amfanin janye tallafin man fetur

0 319

Ministan yada labarai Mohammad Malagi, yace yan Najeriya nan ba da jimawa ba zasu ga amfanin janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya tayi.

Ministan ya bayyana haka jiya yayinda ya karbi bakuncin gwamnan jihar Neja Umar Bago a ofishin sa dake babban birnin tarayya Abuja.

Malagi yace matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin man fetur yana da kyau ga Najeriya.

Ministan ya kuma kara da cewa gwamnatin tarayya yanzu haka ta fara ajiye kudi wanda aka tara bayan an janye tallafi, wanda shine kuma za’a fara rabawa jihohi domin rage radadin halin da ake ciki na janye tallafin man fetur.

Ministan ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu zata amfanar da yan Najeriya karkashin manufofin ta 8 ta tsara baiwa fifiko.

Leave a Reply

%d bloggers like this: