Wannan ya biyo bayan wata wasika da kakakin majalisar Haruna Aliyu ya karanta a zauran majalisar, wacce gwamna Malam Umar Namadi ya aike musu, wacce ta tsallake karatu na daya dana biyu, sannan kuma an mika ga kwamitin majalisar mai kula da kasafin kudi domin ya mata duba na tsanaki ya kuma bada rahotan da ya tattara cikin mako guda.
Idan za’a iya tunawa kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, Babangida Umar, ya fadawa manema labarai a karshen zaman majalisar zartawa na jiha wanda aka yi ranar 16 ga wannan wat ana Agusta cewa, gwamnatin jihar jigawa ta mika bukatar amincewa da Naira Bilyan 44.7 domin a sanya shi cikin kwarya-kwaryar kasafin kudi da za’a gudanar da wasu ayyuka a fadin jihar nan.
A cewar sa Babangida Umar, wannan ne kwaryar-kwayar kasafin kudi na biyu cikin watanni 5, wanda da farko an amince da Naira bilyan 13 a wata Maris,domin gyaran wasu magudanan ruwa, hanyoyi da kuma gadoji a fadin jihar nan. ya ce ana hasashen karin kudaden shiga na daidai da Naira biliyan 44.7 za su samu cikin la’akari da kudaden shigar jihar daga wurare daban-daban tsakanin watan Agusta zuwa Disamba 2023.