‘Nauyi ne a wuyan shugabanni su yi iya bakin kokarinsu wajen kyautatawa jama’arsu duk da karancin kudade’ – Buhari

0 72

Shugaban Kasa Muhammdu Buhari yace nauyi ne a wuyan shugabanni su yi iya bakin kokarinsu wajen kyautatawa jama’arsu, duk da karancin kudade, musamman a yankin yammacin Afrika.

Shugaban kasa ya sanar da haka yau a fadar shugaban kasa dake Abuja lokacin da yake karbar ziyarar bankwana daga jakadan kasar Burkina Faso wanda ya shafe shekara 8 a kasarnan.

Da yake mayar da martani, jakadan ya bayyana fatan alkhari daga kasarsa da shi kansa ga kasar Najeriya, inda ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa huldar diplomasiyya mai kyau wacce ta sanya ‘yan Najeriya ke jagorantar manyan hukumomin kasa da kasa.

Ya kuma bayyana godiya bisa tallafi daban-daban daga Najeriya zuwa Burkina Faso a lokacin ambaliyar ruwa da zaben kasarsu da kuma wasu lokuta da dama na matsi.

Jakadan na Burkina Faso yace yaji dadin zamansa a Najeriya kuma a nan ya haifi ‘yarsa ta karshe, inda ya kara da cewa ba zai taba mantawa da kasarnan ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: