Jam’iyyar PDP ta tsayar da ranar Asabar, 12 ga watan Fabrairun gobe, domin gudanar da taron zaben shugabanninta na shiyyar Arewa maso Yamma.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya ta hannun sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na kasa, Honorable Umaru Bature.

Kamar yadda yazo cikin sanarwar, hakan wani bangare ne na matakan da aka cimma wajen taron shugabannin jam’iyyar PDP na kasa da aka gudanar shekaranjiya Laraba.

Honorable Bature ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron zaben shugabannin jam’iyyar na Arewa maso Yamma a helkwatar jam’iyyar ta shiyyar dake jihar Kaduna.

Sakataren tsare-tsaren ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da dumbin magoya bayan jam’iyyar a shiyyar Arewa maso Yamma da su kasance cikin shiri kuma su kiyaye da ranar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: