Majalisar dinkin duniya tace akalla fararen hula 108 aka kashe a hare-haren jiragen sama a arewacin kasar Habasha cikin makonni 2 da suka gabata.

Ofishin kula da hakkin bil’adama na majalisar dinkin duniya yace an raunata wasu mutane 75 a hare-haren, wadanda ake zargin dakarun sojin saman Habasha ne suka kaddamar.

Gwamnatin tarayyar Habasha tun a baya ta musanta kai hari akan fararen hular yankin Tigray.

Fadar gwamnatin dake Addis Ababa, babban birnin kasar, a jiya ta bukaci shugaban hukumar lafiya ta duniya (WHO), Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, da ya dena magana akan halin da ake ciki a yankin Tigray.

Dr. Tedros, wanda dan asalin kasar habasha, yace an toshe hanyoyin aikawa da magunguna zuwa ga mutanen yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: