Babban jigon jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, a jiya ya sanar da gudunmawar naira miliyan 50 ga al’umomin jihar Zamfara da ‘yan fashin daji suka kaiwa hari a ‘yan kwanakinnan.

Bola Tinubu ya sanar da gudunmawar jim kadan bayan ya jajantawa gwamnan jihar, Bello Matawalle, a Gusau, babban birnin jihar.

Jagoran APC na kasa yayi kiran da a dore da addu’o’i domin shawo kan rashin tsaro a jihar.

Yayin ziyarar zuwa Gusau, Tinubu ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, da tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, da sauransu.

Gwamna Matawalle, wanda ya karbi jigon na APC, yace ziyarar tasa zata karfafa gwiwar al’umomin dake cikin jimami, da ma sauran mutanen jihsar baki daya.

Ya bayyana Bola Tinubu a matsayin dan siyasar da ake bukatar irinsa a Najeriya, shugaba nagari kuma mai hada kan al’umma.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: