NDLEA sun kama wani ɗalibi da kwayar da nauyinta ya kai kilogiram 7.2

0 303

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama wani ɗalibi a filin jirgin saman Abuja bisa zargin yunƙurin fita da kwayar da nauyinta ya kai kilogiram 7.2 zuwa Turai inda yake karatu.

Dalibin mai suna Benjamin Nnamani Daberechi ya ɗaure kwayar Methamphetamine din da busashen kifi a cikin wani buhu.

An kama ɗalibin ne a lokacin da ake binciken kayan matafiya a lokacin da yake dab da hawa jirgi.

Yayin da jami’an hukumar ke masa tambayoyi a kafin kama shi, ɗalibin ya yi ikirarin cewa shi ɗalibi ne da ke karatu a ƙasar Cyprus, to amma da suka fara bincika kayansa sai suka gano kwayar a cikin wani buhu da ya ɗaure busasshen kifi.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ya tabbatar da kamen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: