NSCDC ta Jigawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargin suna lalata wutar lantarkin kauyen Fagam dake karamar hukumar Gwaram
Hukumar NSCDC a jihar Jigawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da lalata layin wutar lantarki a kauyen Fagam da ke Karamar Hukumar Gwaram.
Abubuwan da aka kama sun haɗa da wayoyin aluminium, da falwayoyi, da kayan aiki da babur, inda masu laifin suka ce suna sana’ar gini ne da farauta.
Kwamandan hukumar a jihar, Bala Bodinga, ya ce za a gurfanar da su, tare da shan alwashin ci gaba da kare muhimman ababen more rayuwa.
Ya bukaci jama’a da su ci gaba da ba da bayanai masu amfani domin kare zaman lafiya a jihar.