Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi bane – Gwamnatin Tarayya

0 136

Gwamnatin tarayya ta ce tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ba shugaba ba ne da za a yi koyi da shi a fannin gudanar da mulki da ma sauran harkokin shugabanci.

Gwamnatin ta yi wa Obasanjo wannan kakkausar suka ne a martanin da ta mayar masa na sukar gwamnatin Bola Tinubu da Muhammadu Buhari da ya yi a wata lacca da ya gabatar ta tunawa da marigayi Chinua Achebe a Jami’ar Yale ta Amurka.

A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasar shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya fitar a jiya Litinin, gwamnatin ta soki Obsanjo kan abin da ta ce ya saba na nuna shi gwani ne, tare da bayar da shawarar da ba a nema ba a wajensa, a kan shugabanci da mulki a Najeriya, inda yake ɗora alhakin matsalolin da ƙasar ke ciki a kan waɗanda suka hau mulki bayan gwamnatinsa.

Sanarwar ta yi nuni da irin tarin matsaloli na cin hanci da rashawa da almundahana da keta haddin tsarin mulki da dokoki da gazawar shugabanci da ta ce duk an samu a lokacin gwamnatin Obasanjo da Atiku amma kuma a yau Obasanjon kamar kullum ya kawar da kai daga wannan gazawa ta mulkinsa yana zargin gwamnatocin da suka biyo bayan tashi musamman ta Bola Tinubu da Buhari. Gwamnatin ta ce idan da Obasanjo ya magance yawancin matsalolin da yake suka yanzu a kai, a tsawon shugabancinsa na shekara takwas to da yanzu Shugaban Buhari da Shugaba Tinubu da sun samu sauƙi wajen ƙoƙarin gyara ƙasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: