Za’a dauki matakin kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya

0 133

Gwamnatin tarayya hadi da gwamnonin jihohi za su dauki matakin kafa ‘yan sandan jihohi a mako mai zuwa.

Gwamnan jihar Bayelsa Duoye Diri ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja a jiya Alhamis bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa.

Diri ya bayyana cewa hukumar zabe ta bai wa jihohin Adamawa, Kebbi, Kwara da kuma babban birnin tarayya mako guda wato zuwa 28 ga wannan wata na Nuwamba, kan su bada matsayarsu kan shirin na samar da ‘yan sandan jihohinsu.

Ya ce zuwa lokacin da hukumar zabe ta sake zama mako mai zuwa za a yanke hukunci. A wa’adin na mako guda da aka baiwa jihohi ukun, ya ce Majalisar ta umarci sauran jihohin da suka rage da kuma babban birnin tarayya Abuja su gabatar da nasu a cikin mako guda mai zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: