Osinbajo ya kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki da annobar corona ta lalata

0 98

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki da annobar corona ta lalata wanda za a aiwatar da bashin bankin duniya na dala miliyan 750.

Mataimakin shugaban kasar ya yi bikin kaddamarwar ne a jiya a matsayin share fagen taron majalisar tattalin arzikin kasa da ya jagoranta a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya ce a karkashin shirin wanda zai kasance na tsawon shekaru biyu daga 2021 zuwa 2023 kowace jiha za ta samu dala miliyan 20, yayin da babban birnin tarayya zai samu dala miliyan 15.

A cewarsa, jihohi ne za su tafiyar da shirin kuma za a gudanar da wani shirin na daban da zai binciki sakamakon aiwatar da shirin.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta kuma dauki shirin a matsayin wani muhimmin abin da ya dace wajen kara yawan wadanda za a sanya a shirin tallafawa marasa karfi da kudade.

Mataimakin shugaban kasar ya ce yana sa ran gaggauta aiwatar da shirin a matakin tarayya da jihohi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: