Majalisar Tattalin Arzikin Kasa ta ce har yanzu ba ta yanke shawara kan batun cire tallafin man fetur ba, saboda ana cigaba da tattaunawa.

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya amsa tambayoyi daga manema labaran fadar shugaban kasa bayan kammala taron da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A cewar gwamnan, majalisar ta shafe sama da shekara guda tana tattaunawa kan batun tallafin man fetur.

Ya ce a lokacin da majalisar ta duba wasu bincike a bara, ta gano cewa kasa da kashi daya bisa uku na jihohin kasar nan ne suka cinye kashi biyu bisa uku na tallafin mai fetur.

A cewarsa, a dalilin haka sai batun samun daidaito ya taso.

A nasa bangaren, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su fahimci komai game da dokar masana’antar man fetur, kasancewar NNPC ya zama kamfani mai zaman kansa.

A cewarsa, ayyukan NNPC zasu fara canjawa daga yanzu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: