An samu karin kudaden shiga a shekarar data gabata fiye da na 2020 a jihar Jigawa

0 26

Hukumar tara kudaden shiga ta jihar Jigawa ta ce an samu karin kudaden shiga a shekarar data gabata fiye da na shekarar 2020.

Shugaban hukumar, Ibrahim Ahmad Muhammad Sani ya bayyana haka ta cikin wani shirin Radio Jigawa.

Ya ce Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya sahalewa hukumar kafa kwamati mai wakilai 20 karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Malam Umar Namadi da kwamishinan kudi da wasu domin kawo managartan tsare-tsare da zasu inganta harkokin tara kudaden shiga.

Ibrahim Sani ya kara da cewa ta hanyar bullo da asusun bai daya, gwamnati ta bunkasa wajen tara kudaden shiga fiye da kashi 70 cikin 100, inda ya ce hukumar na cigaba da bullo da sabbin tsare-tsaren tara kudaden shiga ta kafar sadarwa ta zamani domin ayyukan hukumar su dace da zamani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: