Manyan limaman fadar Vatikan za su rasa wani kaso na albashinsu don biyan wasu kananan ma’aikata a cewar shugaban darikar Katolika. Matakin ya boyi bayan rashin samun kudaden shiga da fadar ke yi saboda annobar corona.

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya umarcin manyan limaman fadar Vatikan su zaftare albashinsu da kashi 10 cikin 100 a wani mataki na kare aikin wasu ma’aikata a fadar a lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki saboda corona.

Wata sanarwa daga fadar Vatikan na cewa umarnin Paparoman na zaftare albashin limaman fadar zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afirilu, sai dai matakin ba zai shafi kananan ma’aikata ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: