PDP Ta Fadi Dalilin Da Ya Sa Buhari Ya Ki Baiwa Osinbajo Mulki

0 118

Wasu masu sharhi na ganin rashin baiwa mataimakin shugaban kasa daman rike kasar yayin da shugaban ke duba lafiyarsa a Ingila, ka iya shafar dangantakarsu.

‘Yan jami’iyar adawa suna gani akwai yiwuwar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ka iya taka rawar gani fiye da Shugaba Buhari ne ya sa ba a ba shi rikon kasar na wucin gadi a lokacin da shugaban kasar zai je ganin likitocinsa a Ingila ba.

A hirarsa da Muryar Amurka Malam Garba Shehu ya ambato dokar Najeriya da ke cewa dole shugaban kasa ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa idan zai bar kasar sama da kwanaki 21, amma ya ce shugaba Buhari ba ma zai kai kwanaki 20 a wannan ziyarar duban lafiyarsa ba a Landan.

Ya kuma kara da cewa idan shugaban ya yi abin da ya sabawa doka ko majalisar dokoki za ta iya mika ragamar mulkin ga mataimakinsa.

Sai dai akwai masu ganin rashin baiwa mataimakin shugaban kasa daman rike kasar yayin da shugaban ke duban lafiyarsa a Ingila ka iya shafar dangantakar shugaban da mataimakinsa, batun da Malam Garba Shehu musunta.

Ya ce kyakkyawar dangantaka dake tsakanin shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbanjo tana nan daram kuma wannan ba zai bata tsakanin su ba saboda suna aiki tare da yarda da aminci dan haka ya ce bai ga wani dalilin da zai sa mutane su yita fargaba ba.

Malam Shehu ya yi fatali da abin da wasu ke tunani cewa kila mataimakin shugaban na da wata gazawa ne shi ya sa shugaban kasa bai bar masa riko ba.

Ya ce babu wani takamaiman aiki da doka ta ware wa mataimakin shugaban kasa sai wasu ‘yan kalilan da shugaban zai umarce shi da ya yi kuma babu wanda ya san abin da suka yi tsakaninsu dan haka bai yiwuwa a ce mataimakin nadawata gazawa.

A bangaren ‘yan adawa suna gani an shirya ne domin tabbatar da ganin cewa Yemi Osinbanjo bai sake rike mulki na wucin gadi ba kamar yadda aka yi a baya.

Rahoton VOA:

https://www.voahausa.com/a/pdp-ta-fadi-dalilin-da-ya-sa-buhari-ya-ki-baiwa-osinbajo-mulki/5836500.html

Leave a Reply

%d bloggers like this: