Yan sanda a Kano suna cafke da Awaisu Auwalu,dan shekara 40, mazaunin unguwar Samegu da ke cikin garin Kano, saboda ya lakadawa dan nasa duka har lahira kan zargin satar galan galan biyu na manja a cikin shagon da yake sayar da kayan masarufi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, yayin tabbatar da afkuwar lamarin ya ce, Awaisu ya yi amfani da sanda ya bugi dansa mai shekaru 19, Auwalu Awaisu har lahira.

Haruna Kiyawa, ya ce bayan samun rahoton, an garzaya da wanda aka azabtar zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda ya mutu a ranar Litinin da misalin karfe shida lokacin da yake karbar magani a asibitin.

A yayin bincike, mahaifin ya furta cewa ya yi wa dan nasa bulala, inda ya yi zargin cewa marigayin ya yi sata da yawa daga shagon nasa.

Kiyawa ya kara da cewa “Amma, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ba da umarnin a tura karar zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar, sashin kisan kai don gudanar da bincike na hankali”

A cewar PRO, za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: