Na’urar da ke hango zirga-zirgar jirage da tuntuɓarsu wato radar ta kasa ganin inda wani jirgin rundunar sojin saman Najeriya ya shiga, a cewar sanarwar rundunar.

Jirgin yaƙin yana kan wani aiki ne na taimakon dakarun rundunar sojin ƙasa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce an daina jin ɗuriyar jirgin ne tun ƙarfe biyar na yammacin Laraba 31 ga watan Maris.

“Har yanzu babu wasu bayanai kan inda jirgin ya shiga ko dalilin ɓacewarsa, amma za mu sanar da al’umma da zarar mun gano wani abu,” a cewarsa.

Aikin da jirgin ke yi wani ɓangare ne na ci gaba da yaƙi da ƴan ƙungiyar Boko Haram da ake yi.

Rundunar ba ta kuma yi bayani kan ko mutum nawa ne ke cikin jirgin ba.

Jaridar Punch ta ruwaito wani tsohon kwamanda a rundunar sojin saman ƙasar na cewa “idan har aka yi minti 30 ba a ji ɗuriyar jirgin yaƙi ba to za a ayyana cewa wannan jirgi ya ɓata ne.”

A watan Fabrairun da ya gabata ma wani jirgin yaƙin rundunar sojin saman ƙasar ya yi hatsari a Abuj kan hanyarsa ta zuwa Minna, inda dukkan jami’ai bakwai da ke cikinsa suka mutu.

Asalin Labarin: https://www.bbc.com/hausa/labarai-56600999

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: