Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya bayar da gudummuwar naira milyan ashirin ga mutanen da iftila’in gobara ya afka musu a babbar kasuwa ta jihar katsina.
Gwamnan ya bayyana gudummawar ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari tare da takwaran sa na Jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu wanda shima ya bada makamanciyar gudummuwa ga yan kasuwar.
Da yake jawabi, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya ce sun zo jihar Katsina ne dimin su jajantawa Gwamnan da kuma yan kasuwar da sukayi asarar kaya na miliyoyi sakamakon gobarar da akayi satin da ya gabata.